Bankin Duniya ya ce Najeriya da sauran kasashen Kudu da Saharar Afirka, sun gaza cimma muradin rage matsalar tsananin talauci a tsakanin al’ummominsu a shekarar 2022.
A cikin sabon rahotonsa kan binciken batutuwan da suka shafi makomar tattalin arzikin Afirka, Bankin Duniyar da ke Washington ya ce aiwatar da matakan rage fatara, tsakanin al’ummar Kudu da Saharar Afirka ya cigaba da tafiyar hawainiya, wanda dama tuni barkewar cutar Korona ta haifar da kawo cikas tsare tsaren rage talaucin.
Bankin ya kara cewa annobar ta Korona ta haifar da dogon tasiri kan ci gaban da aka dade ana kokarin cimma a kasashe masu tasowa, matsalar da ta fi shafar matalauta ta hanyar kara musu nauyin wahalar da suke ciki.
A bangaren Najeriya kuwa, rahoton ya ce rashin karsashin da tattalin arzikin kasar wajen farfadowa daga tasirin annobar Korona, ya gaza kawar da matsalar ayyukan yi da kuma asarar kudaden shigar da kasar ta fuskanta.
A makon da ya gabata Bankin Duniya ya wallafa wani rahoto da ke gargadin cewa ‘yan Najeriya fiye da miliyan 60 ka iya rasa guraben ayyukansu nan da shekara ta 2030, muddin gwamnati ba ta dauki matakan da suke dace wajen kaucewa aukuwar hakan ba.