Kotu ta sake hana DSS cafke gwamnan CBN, Godwin Emefiele

0
108

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kawo cikas ga kokarin da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ke yi na kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan zargin daukar nauyin ta’addancin.

A hukuncin da alkalin kotun Mai Shari’a J.T Tsoho ya yi kan karar da kungiyar Incorporated Trustees of Forum for Accountability and Good Leadership ta shigar domin neman a dakatar da DSS daga cigaba da barazanar kama Emefiele balle musguna masa ko bata shi.

Alkalin ya kuma dakatar da SSS da ko ma waye daga kokarin kamu ko gayyaya ko tsare gwamnan na CBN kan zargin tallafawa ta’addanci ta bangaren kudade tare da kyaleshi ya gudanar da ayyukansu a matsayin gwamnan CBN muddin ba wai umarnin suka samu daga wata babbar kotu ba.

Kotun ta ce a kyale gwamnan ya samu cikakken damar gudanar da ayyukan da suke gabansa ba tare da firgitashi ko tada masa hankali ba.

Kafin wannan ma, wata kotun ta yi watsi da bukatar DSS inda ta ce hukumar ta koma ta samo kwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake dawowa gabanta kan batun.

Ita dai DSS na zargin Godwin Emefiele, da tallafawa ta’addanci da kudade hakan ya sabawa doka ya kuma aikata laifi kan tattalin arziki.