Pelé a Afirka: Bajinta da tarihi da maganganun da ake laƙaba masa

0
111

Kasancewarsa daya daga cikin manyan taurarin matasan bakaken fata a fagen wasanni a zamanin talabijin, Pelé ya samu karbuwa da kauna daga ‘yan Afirka a fadin nahiyar.

A lokacin da kasashen Afirka ke fafutukar samun ‘yancin- kai a karshe-karshen shekarun 1950 da kuma farko-farkon 1960, Pelé ya rika samun gayyata daga kasashen Afirka da suka samu ‘yanci, domin wasan sada zumunta da kungiyarsa Santos FC da kuma tawagar kasarsa ta Brazil.

A tarihinsa da ya rubuta, Pelé ya bayyana cewa wadannan tafiye-tafiye da ya rinka yi zuwa kasashen Afirka a wannan lokaci ba kawai sun sauya yadda yake kallon duniya ba har ma da yadda ya ce duniya ta dauke shi.

Mutumin da ya rubuta kundin kungiyar kwallon kafa ta Santos, Guilherme Nascimento, ya yi daidai kamar yadda ya nuna cewa wadannan tafiye-tafiye zuwa Afirka na cike da labarai wadanda kusan da wuya a iya bambancewa tsakanin na gaskiya da kuma na kunne-ya-girmi-kaka.

Zuwan Pelé Algeria, a misali ya kasance kamar wani abu na fim. A shekarar 1965, tauraron wanda a lokacin yana da shekara 24 ya je kasar a daidai lokacin da darektan fim, Gillo Pontecorvo yake hada fim din ”The Battle of Algiers”.

A don haka sai abin ya zo daidai da lokacin da za ka ga tankokin yaki suna ta kai-komo a fadin kasar kama daga kauyuka zuwa Casbah.

Shugaban kasar na wannan lokaci Ahmed Ben Bella, mai matukar sha’awar wasan kwallon kafa ya shirya wasan sada zumunta biyu domin wannan ziyara.

Daya a Oran a ranar 15 ga watan Yuni, dayan kuma a babban birnin kasar, Algiers, bayan kwana hudu.

Sai dai kuma ministan tsaro na lokacin Houari Boumediene ya yi juiyin mulki inda ya hambarar da Shugaba Ben Bella, saboda haka ya soke daya wasan sada zumuntar.

Wasu ‘yan jarida da fashin baki sun ce ministan ya yi amfani da yanayin da ake ciki na ruguguguwa da murnar zuwan tauraron kwalon kafar, a matsayin wata hanya ta dauke hankali ya yi juyin mulkin.