New York ta amince a rinƙa mayar da gawarwaki ɓurɓushin ƙasa

0
156

Jihar New York ta zama jihar Amurka ta baya-bayan nan da za ta bayar da dama a rinƙa mayar da gawarwaki ƙasa.

Hakan na nufin mutum zai iya bayar da umarni a mayar da gawarsa ƙasa idan ya rasu – wanda wasu ke ganin hakan yana da kyau ga muhalli maimakon a binne mutum ko kuma a ƙona gawarsa.

Idan za a yi hakan, akan saka gawar mutum ne a cikin wani akwati a rufe shi tsawon makonni domin gawar ta ruɓe bayan an gauraya ta da wasu abubuwan da za su taimaka ta zama ƙasa.

A 2019, Washington ta zama jihar Amurka ta farko da ta halasta wannan lamari. Sai kuma daga baya Colarado da Oregin da Vermont da California suka biyo baya.

Hakan na nufin New York ta zama jiha ta shida a Amurka da a hukumance ta amince da hakan bayan gwamnan New York, Kathy Hochul a ranar Asabar ya saka wa dokar hannu.

Ana saka gawar a cikin wani ɗan dogon ƙwarya-ƙwaryan sunduƙi sa’annan ana jefa wasu abubuwa a ciki kamar irin su dusar katako da da ciyawa da wasu furanni inda a hankali gawar take ruɓewa ta gauraye da suaran abubuwan da ke haɗe da gawar.

Bayan kimanin wata guda – da kuma ɗumama gawar domin kashe duk wani abu da zai iya zama ƙwayar cuta, ana ɗaukar ƙasar da gawar ta zama domin bai wa iyalan mamacin.

Za a iya amfani da ƙasar wadda ta samo asali daga gawa domin shuka bishiyoyi ko furanni ko kayan lambu.

Wani kamfanin Amurka mai suna Recompose ya ce aikin da yake yi zai iya rage sinadarin carbon mai ɗunbin yawa idan aka kwatanta da ƙona gawa.

Fitar da sinadarin carbon na daga cikin abubuwan da suke jawo sauyin yanayi sakamakon suna ɗaure yanayin zafin da duniya ke da shi.

Haka kuma binne mutum a cikin akwatin gawa wanda ake yin sa da katako shi ma yana jawo asarar katako da kuma ainahin filin da ake rufe mutum da sauran albarkatun ƙasa.

Kamfanin ya ce matakin mayar da gawar mutum ƙasa yana da amfani matuƙa ba wai don kiyaye muhalli kawai ba, amma don samun sauƙi a biranen da ake ƙarancin maƙabartu domin binne mutane.