Wadanda suka kai wa ayarina hari za su dandana kudarsu – Tambuwal

0
101

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocinsa, inda ya ce za a gurfanar da wadanda suka kai harin.

Tambuwal ya shaida wa manema labarai a wajen taron masu ruwa da tsaki da suka yi da masu rike da mukaman siyasa a jihar, cewa an kama wasu daga cikin maharan kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kuliya.

“Hukumomin tsaro na binciken lamarin. An dai kama wasu. Kuma an tabbatar da cewa doka za ta yi aiki,” in ji gwamnan.

Tambuwal ya ce: “Abin takaici ne jiya a hanyarmu ta dawowa daga Wammako, a ofishin Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, wasu ‘yan iska sun kai hari kan ayarina a kan hanyarmu ta zuwa gidan gwamnati.

“Ba za mu lamunci duk wata al’ada ta tashin hankali a Jihar Sakkwato ba,” in ji gwamnan.

“Don haka ina kira ga daukacin shugabannin siyasa na Sakkwato da su guji tashin hankali; sannan kuma su shawarci dukkan mabiyansu da magoya bayansu da su fita yakin neman zabe cikin lumana; kuma kada a yi tashin hankali.

“Kamar yadda aka sani, mun yi imani da zaman lafiya. Muna kira da a zauna lafiya a Jihar Sakkwato, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyyun siyasa, nasaba ko ra’ayi ba.