Sojan fadar shugaban kasa ya bude wa ‘yan acaba wuta, ya kashe fasinja

0
126

Wani jami’in sojan Nijeriya, Abubakar Idris, da ke aiki a karkashin rundunar tsaron fadar shugaban kasa, ya bude wuta kan wasu ‘yan acaba a Abuja, inda ya kashe wani fasinja nan take.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare a kan gadar da ke kusa da hanyar Aguiyi Ironsi a Asokoro, inda shi da abokan aikinsa suke gadi.

Wata majiya ta shaida cewar an dauke mamacin zuwa asibitin gundumar Asokoro, domin sake tabbatar da mutuwarsa.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce, “Dakarun da ke gadin a daren ranar Lahadi, sun hangi wasu ‘yan acaba sun doso kusa da kan gadar da suke gadi.

“Sojan ya yi kokarin tsayar da wani matukin babur wanda ke goye da fasinja, a kan hakan ne ya bude musu wuta, fasinjan ya mutu nan take, matukin mashin din da sauran sun gudu bayan da lamarin ya faru.”

Ya kara da cewa, “Nan take ba tare da bata lokaci ba, sojojin suka bar wajen tare da barin gawar a wajen. Sai da wasu jami’an ‘yan sanda sun dauke gawar. Nan take suka kai gawar zuwa asibitin Asokoro.”

Kakakin rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasa, Abakpa Godfrey, ya ce bai da masaniya kan faruwar lamarin.

Ya ce, “Ba zan iya tabbatar da wannan lamarin ba. Ba na nan yanzu nake dawowa Abuja, don haka ban da masaniya a kai.