Majalisar masarautar Bauchi ta amince da tsige Alhaji Muhammadu Bello Kirfi daga mukaminsa na dan majalisar bisa abin da ta bayyana a matsayin rashin biyayya da kuma rashin mutunta gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.
Wasikar tsige Kirfi wanda ke rike da mukamin Wazirin Bauchi mai kwanan wata Talata 3 ga watan Janairu, 2023 mai dauke da sa hannun sakataren majalisar Alhaji Shehu Mudi Muhammad ta ce: “An umurce ni da in koma ga wata wasika da aka samu daga ma’aikatar. Al’amuran Kananan Hukumomi tare da Nuni: MLG/LG/S/72/T mai kwanan wata 30th Disamba, 2022.
“Abin da ke cikin wasikar ya nuna rashin biyayyarku da rashin mutunta Gwamnan Jihar da gwamnati. Don haka, ya ba da umarnin cire ku tare da sakamako nan take.