DSS ta cafke mutum 2 kan zargin tayar da bam yayin ziyarar Buhari jihar Kogi

0
119

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da tayar da bam a mota a ranar 29 ga Disamba, 2022, kusa da fadar Ohinoyi na Ebiraland a Okene, jihar Kogi.

 

Ku tuna cewa fashewar ta faru ne jim kadan gabanin ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

 

Wadanda ake zargin dai sun hada da Abdulmumin Ibrahim Otaru wanda akafi sani da Abu Mikdad da kuma daya daga cikin abokansa, Saidu Suleiman.

 

Mai magana da yawun hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 3 ga watan Janairun 2023, kuma Otaru ya samu rauni a kafarsa ta hagu yayin da yake kokarin tserewa.