Kotu ta dakatar da DSS kan cafke shugaban hukumar INEC

0
105

Wata babbar kotu da ke babban birnin tarayya Abuja ta hana tsige shugaban zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga matsayinsa bisa zargin kin bayyana kadarorinsa.

Mai shari’a M.A. Hassan a ranar Laraba ya ki bukatar  tare da tara 14 da masu shigar da karar suka kawo.

Ya hana jami’an tsaro na farin kaya (DSS), ‘yan sandan Nijeriya, da kuma kotun da’a (Code of Conduct Bureau) kama Farfesa Yakubu.

A karar da Somadina Uzoabaka ta shigar da babban lauyan gwamnatin tarayya da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Yakubu mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 tana neman kotun ne da ta tilastawa Farfesa Yakubu sauka daga kan mukaminsa kan zargin kin bayyana kadarorinsa ta yadda doka ta tanadar.