2023: ‘Yan damfara sun bude manhajar intanet don daukar ma’aikatan zabe – INEC

0
159

Wani gargaɗin baya-bayan nan daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ja kunnen jama’a cewa ba ta san da zaman wata manhajar da wasu ‘yan damfara su ka buɗe da sunan ɗaukar ma’aikatan zaɓe na wucin-gadi ba.

Sakataren Yaɗa Labaran INEC, Rotimi Oyekanmi ne ya yi wannan gargaɗin, ranar Talata a Abuja.

Ya ce tuni INEC ta rufe shafin manhajar ta na ɗaukar ma’aikatan zaɓe, kamar yadda ta yi bayani a baya.

A cikin Satumba ne dai INEC ta yi sanarwar cewa za ta buɗe shafin manhajar a ranar 14 ga Satumba, 2022 ta rufe a ranar 14 ga Disamba, 2022.

“Wannan shafin manhaja na intanet, na bogi ne, ba na INEC ba ne. Saboda an rufe shafin manhajar INEC na ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi, tun a ranar 14 ga Disamba, 2022.