A bisa kokarin tabbatar da samun nasarar jam’iyyar APC a zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari, zai raka tawagar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da za a gudanar a jihohi 10.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da daraktan kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar, Festus Keyamo ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, jihohi 10 sun hada da, Adamawa wadda za a je a ranar 9 ga watan Janairu; Yobe a ranar 10 ga watan Janairu; Sakkwato a ranar 16 ga watan Janairu, sai Jihar Kwara a ranar17 ga watan Janairu, 2023.
Sauran jihohin sun hada Ogun a ranar 25 ga watan Janairu, Kuros Ribas a ranar 30 ga watan Janairu, Nasarawa a ranar 4 ga watan Fabrairu, Katsina a ranar 6 ga watan Fabrairu, Imo a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan a karkare gangamin a Jihar Legas a ranar 18 ga watan Fabrairu.
Shugaba Buhari, a baya dai ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben Tinubu a garin Jos a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2022.
Sai dai, kafin a fitar da wannan sanarwar, ba a ga shugaban kasar ya halarci sauran gangamin yakin neman zaben dan takarar da aka gudanar a baya-bayan nan ba.