Rahoto: Amurka ta saba amfani da annoba a matsayin makami

0
121

A cikin kwanaki talatin da suka gabata, kasar Sin tana kara kyautata matakanta na kandagarkin annobar cutar COVID-19, amma aka sake jin yadda wasu na zargi kamar yadda suka saba, musamman ma daga kasar Amurka. Daga muhimman bayanan da aka tattara kan yanayin da Amurka ke ciki tun bayan barkewar cutar shekaru uku da suka gabata, an gano cewa, Amurka ta saba yin amfani da annoba a matsayin makami na zargen sauran kasashe.

Duk da cewa, gwamnatin Amurka ta kan takali matakai na kimiyya, amma yunkurinta shi ne mayar da annoba a matsayin makami, inda ta shafawa kasar Sin bakin fenti wai kwayar cutar ta samo asali ne a kasar Sin, wani lokaci ma ta kan nuna damuwa cewa, akwai yiyuwar samun sabon nau’in kwayar cuta a kasar Sin.

Amurka dai na ganin cewa, yaduwar annoba ba lamarin kiwon lafiyar jama’a ba ne, a maimakon haka, tana amfani da cutar ce a matsayin wani makami na siyasantar da annoba, wannan shi ne babban dalilin da ya sa kasashen duniya suke shan wahalar dakile yaduwar annobar.

(CMG Hausa)