Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta sanar a ranar Asabar din da ta gabata cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba da ke dakon shiga jirgin kasa daga Igueben da ke karamar hukumar Igueben a jihar zuwa Warri a jihar Delta.
Rundunar, a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta, Chidi Nwabuzor, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin makiyaya ne dauke da bindigogi kirar AK-47, sun kutsa kai cikin tashar jirgin inda suka yi ta harbin iska, kafin daga bisani su garzaya da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba.
Sanarwar ta kara da cewa, ana cikin haka ne wasu daga cikin fasinjojin suka samu raunukan harbin bindiga, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, an fara aikin ceto wadanda aka yi ma raunuka da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.