Illar raba kan mata 2

0
165

Babbar illar raba kan mata da wasu Magidanta suke yi ba karama bace, wadda take kawo matsalar da zata iya shafar rayuwar duk wadanda suke gidan baki daya.

Domin kuwa matukar shi maigidan da ya tara dukkan matan da suke gidan idan bai gyara halin sa na yin abubuwan da basu dace ba, don kawai ya farantawa ita amaryar zuciyarta,to abin fa daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba.

Idan aka yi rashin sa’a har ita uwragidan ta fita a sanadiyar haka ko shi mijin ya sake ta,ko kuma taga cewar ba zata iya jure ma zaman gidan ba, a irin wannan yanayin ta yi tafiyarta.

A karo na farko matsalar da shi maigidan zai fara fuskanta ko su ‘ya’yanta ita ce ta kula da tarbiyyarsu kamar yadda mahaifiyar su take yi masu,saboda ba dole bane kishoyinta ko kishiyarta su yi ma ‘ya’yan tarbiyyar yadda mahaifiyarsu take yi masu data dace.

Wannan ya nuna kenan maganar gaskiya ba ance wasu ba za su iya tarbiyyar ‘ya’yan wasu ba ne,amma abin kallo anan shi ne,wasu da biyu ne, da gangan za su yi ta ingiza su suna sa su hanya ko hanyoyin da tarbiyarsu za ta gurbace wanda abin daga karshe su kasa amfanar su kansu da ma masu hulda da su kai tsaye ko a kaikaice.