Hakikanin abun da ya kai Atiku kasar Ingila

0
124

Daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Dino Melaye ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya je birnin Landan na kasar Birtaniya ne domin ganawa da gwamnatin Birtaniya.

Akwai rahotannin da ke cewa Atiku yana Landan don jinya amma Melaye ya bayyana rahotannin a matsayin ‘kanzon kurege’.

“Ku yi watsi da karyar makaryata da suka gaza tuba. Atiku yana cikin koshin lafiya dari-bisa-dari. Gwamnatin Birtaniya ce ta gayyaci dan takarar shugaban kasar, Atiku Abubakar, kamar yadda suka gayyaci Bola Tinubu da Peter Obi a baya,” kamar yadda Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.