Aisha Bichi ta ba da umarnin a kamo mata Abba gida-gida

0
275

Matar shugaban SSS ta umarci jami’ai su kama Abba Kabir, kuma su hallaka guda cikin hadimansa.

Aisha Bichi, wacce mata ce ga shugaban hukumar tsaron farin kaya (SSS), Yusuf Bichi, tayi umarnin a kama dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) domin hana shi hawa jirgin Max Air daga Kano zuwa Abuja a daren ranar Lahadi, sakamakon tsaiko da tawagar Abba ta janyo a filin sauka da jiragen sama na Malam Aminu Kano dake Kano.

Wani Rahoto da jaridar Daily Nigerian ta fitar, ya bayyana cewa, tsaikon ya bata ran ita Aisha, lamarin da yasa jami’anta suka fara dukan mutane da ababen hawa bisa rashin girmama Madam, har sai da shi Abba ya shiga dakin jira ya same ta tare da korafi bisa abinda jami’an tsaro suka aikata ga mutanensa.