Yadda aka tabka mummunar asara a gobarar kasuwar Poteskum ta jihar Yobe

0
288

An yi asarar kadarori na miliyoyin naira sakamakon barkewar gobara a babbar kasuwar Poteskum da ke jihar Yobe.

An ce, gobarar ta tashi ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8 na dare.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, gobarar ta lalata kadarori na miliyoyin Naira a sassan kasuwar ‘yan gwanjo da ‘yan doya da ‘yan keke da kuma shagunan (POS) na kasuwar.

Kawo yanzu dai ba a gano ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton, domin an ce kasuwar babu wutar lantarki a lokacin da lamarin ya faru.

An tattaro cewa samari nagari ne suka kashe gobarar sakamakon rashin zuwan jami’an kashe gobara da ke Poteskum da kuma jami’an da ke makwabtaka da ita.