Shugaba Buhari ya bude wasu manyan aiyuka 6 a jihar Yobe

0
123

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bude wasu muhimman ayyuka guda shida da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samar a ziyarar yini daya da ya kai jihar Yobe ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya sauka a babban filin jirgin saman kasa da kasa na Damaturu, tare da tawagarsa inda ya samu tarba daga Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni tare da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da shugaban majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan da sauran manyan kusoshin gwamnati a jihar.

Shugaban ya fara da bude filin jirgin saman Damaturu wanda gwamnatin Mai Mala ta samar da sabuwar Shalkwatar Rundunar Yan-sanda a Damaturu da kuma Asibitin ‘Yansanda da makaranta a hade, wadanda gwamnatin Tarayya ta gina a jihar.

Shugaba Buahri, ya kuma bude katafariyar cibiyar kula da lafiyar mata da yara mafi girma a Nijeriya, wadda gwamnatin jihar Yobe a karkashin Gwamna Buni, a cikin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu ta samar.

Bugu da kari, Shugaban ya kuma bude babbar kasuwar zamani wadda gwamnatin jihar ta gina a Damaturu da sabbin rukunan gidaje a wurare daban-daban a Damaturu da Shalkwatar kananan Hukumomi 17 da ke fadin jihar, sauran aiyukan sun hada da sabuwar makarantar zamani ta musamman a rukunin gidaje na New Bra-Bra duk a birnin Damaturu.