NIS ta hukunta jami’ai 36 da aka kama da laifuka

0
119

Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta kori wasu jami’ai 4 da rage wa wasu 14 muƙami sakamakon laifukan da suka aikata daban-daban, a wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi wajen tsame bara-gurbi da kuma ƙarfafa yaƙin da Gwamnatin Tarayya ke yi da cin hanci da rashawa.

Kwamitin da hukumar ta kafa na ladabtarwa ne ya yanke musu wannan hukuncin.

Har ila yau, bayan kammala ƙwaƙƙwaran bincike, kwamitin ya wanke wasu jami’ai huɗu, kana an sauya wa wasu biyu wurin aiki, sannan akwai wasu 11 da aka ba su takardar gargaɗi. Har ila yau, akwai wani jami’i da aka yi masa ritayar dole, kana akwai wasu 11 kuma da ke jiran shari’a.

Shugaban Hukumar ta NIS, CGI Isah Jere Idris ya sake bai wa al’umma tabbacin cewa babu wasu shafaffu da mai a NIS domin duk wanda ya yi laifi za a hukunta shi. Haka nan ya yi kira ga jama’a su ƙara kula da ba da goyon baya ga hukumar domin ta ji daɗin sauke nauyin da ke wuyanta ga ‘yan ƙasa da sauran abokan hulɗa ta hanyar miƙa ƙorafi ta waɗannan hanyoyin:
(a) lambar waya: +2348033074681; +2348021819988
(b) twitter: @nigimmigration
(c) email: [email protected]

Jami’in yaɗa labarai na hukumar ta NIS, DCI Tony Akuneme ya fitar da sanarwa kan hukunce-hukuncen da hantsin yau Talata.