Shugaban DSS ya yi magana kan rikicin matar sa ​​da Abba gida-gida da ya barke a Kano

0
98

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi, ya ce makiya ne ke kokarin bata masa suna da iyalansa sabida kin amincewarsa kan sauya wasu muhimman batutuwan mulki da harkokin kasa.

Bichi ya zargi kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu wurin shirya wannan makircin ta hanyar gudanar da tarukan manema labarai, zanga-zanga akan tituna don bata masa suna.

A baya mun rahoto muku cewa an samu sabanin rashin fahimta a ranar Lahadi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) tsakanin uwargidan shugaban hukumar DSS, Aisha Bichi, uwargidan shugaban DSS da Abba Gida-gida yayin da uwargidan ta hana Abba Yusuf dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar NNPP hawan jirgi.

Rikicin dai ya samo asali ne bayan da ayarin motocin Abba Gida-gida suka kawo wa ayarin Uwargida Aisha Bichi tsaiko wajen shiga dakin manyan baki na filin jirgin (VIP), lamarin da ya sa jami’an tsaronta shiga cikin lamarin don bude hanyar, lamarin da ya kai ga cece-ku-ce tsakanin jami’an tsaro da mataimakan dan takarar gwamnan.

Amma da yake mayar da martani kan lamarin ta bakin mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ta wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Talata, babban jami’in leken asirin ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta bankado tsare-tsare da wasu ‘yan siyasa da wasu ‘yan bangar siyasa da ke cikin gwamnati da wajenta ke kokarin daukar nauyi don bata masa suna.

A cewarsa, babu wani batanci da cin zarafi da zai hana hukumarsa gudanar da ayyukanta, ya kara da cewa, Hukumar ba za ta sa ido ta kyale duk wani gungun ‘yan bangar siyasa ba da basu gamsu da ayyukan hukumar ba su kawo cikas wajen hana hukumar gudanar da ayyukanta.