Gwamnatin Yobe ta sanya wa kasuwar Nguru sunan Shehu Gibrima

0
87

Gwamnatin Jihar Yobe, bisa jagorancin Mai Mala Buni ta sanya wa sabuwar kasuwar da ta kammala ginawa a garin Nguru a jihar (Nguru International Modern Market), sunan Shehun Malamin addinin musuluncin nan Shehu Muhammad Gibirima.

A sanarwar manema labaru, mai dauke da sa-hannun Darakta-Janar kan hulda da ‘yan jaridu da kafafen yada labarai a ofishin Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, da yammacin ranar Alhamis, Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakoncin Malama Aisha AbdulMutalib, ‘yar asalin garin Potiskum, wadda da ta yi nasarar zama gwarzuwa a gasar karatun Alkur’anin Mai Tsarki (rukunin mata) a garin Gusau ta jihar Zamfara.

Gwamna Buni ya bayyana cewa ya sanya wa kasuwar sunan Shehin Malamin ne domin tunawa da gagarumar gudummawar da ya bayar wajen yada addinin musulunci a wannan nahiyar.

“Sannan kuma a matsayin sa na Malamin Addinin musulunci a fadin duniya, wanda al’ummar musulmin duniya ke girmamawa, bisa gudumawar da ya bayar.” In ji Buni.

Dangane da gwarzuwar gasar Alkur’anin kuwa, Gwamna Buni ya bayyana jindadinsa dangane da kokarin Malama Aisha, inda ya nunata a matsayin abin alfahari ga jihar Yobe.