Mbappe ya ki zuwa Liverpool saboda Madrid

0
247

Paris St-Germain tace a kakar wasanni da ta gabata ta shirya barin dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, ya koma Liverpool amma ya yi watsi da batun, saboda rahotanni dake alakanta shi da komawa Real Madrid. 

West Ham ta yi tayin sayen dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Danny Ings, mai shekara 30, da nufin karfafa gabanta yayin da kungiyar da yanzu haka ke fuskantar barazanar ficewa daga gasar ke fafutukar neman cin kwallaye.

West Ham ta yi kokarin dauko dan wasan bayan Ingila Harry Maguire, mai shekara 29, a matsayin aro amma kocin Manchester United Erik ten Hag ya ki amincewa da yunkurin nasu, wanda ke kokarin ci gaba da rike kyaftin din kulob dinsa a Old Trafford har zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Mail)

Everton za ta yi wani yunkuri maye gurbin kocinta Frank Lampard, mai shekara 44, da tsohon kocinta David Moyes, mai shekara 59, duk da barazar da dan asalin Scotland din ke fuskanta a West Ham, yayin da  kungiyoyin biyu ke fuskantar koma baya a Premier League. (Sun)

Moyes zai fuskanci kora idan West Ham ta yi rashin nasara a wasansu da Everton a filin wasa na London ranar Asabar.

Manchester United tabi sahun Real Madrid wajen zawarcin dan wasan Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 18, wajen tayen bashi albashi mai soka.