Tun lokacin da aka sanya hannu a dokar zabe da ake yi wa kuskwarima ta shekarar 2022 har ta zama doka, mutane suka fara hasashen cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta iya gudanar da ingantaccen zabe wanda ba a taba irinsa ba a tarihin Nijeriya.
Ko da ma aka samu rahoton rashin tsaro zai iya sanyawa a dage zabe bai sauya tunanin shugaban hukumar ba. Mutane ma dai sun san cewa wannan ba huruminsa ba ne, akwai dan abu kadan da hukumarsa za ta iya yi.
Hukumar tana da wasu kalubale a tsare-tsarenta, amma wadannan matsaloli an magance su kuma zai iya faruwa a kowani lokaci, kuma a kowacce kasa. Matsalar da ake fama da shi wanda ya kamata INEC ta duba shi ne, yadda ‘yan siyasar Nijeriya suke zuzuta dabi’ar nan ta siyasar kabilanci da addini.
Sashi na 97 na dokokin zaben shekara ta 2022, ya zayyano cewa haramun ne yin yakin neman zabe a kan addini ko kabila. Dokar ta ce: duk dan takara koko wani mutum ko wata kungiya suka yi yakin neman zabensu a kan addini ko kabilanci ko bangaranci don sun tallata jam’iyyarsu ko su soki wani bangare ko dan takara sun aikata laifi a karkashin wannan sashi(a), wanda zai biya mafi yawan kudi na Naira miliyan 1,000,000 ko kuma a daure shi a gidan yari na tsawon shekar 12 ko kuma a hada mashi su gaba daya, sashi (b) idan kuwa jam’iyyar siyasa ta aikata wannan za ta biya mafi yawan kudi na Naira miliyan 10,000,000.
Wannan matsalar a nan idan aka danganta da jam’iyyar APC, wadanda suke amfani da wannan dama na cewa sun bayar da tikitin takararsu ga wadanda suke addininsu guda. A dokance kowa zai iya zabar wadanda suke addini guda don ma an yi a baya can, kenan wannan ba sabon abu ba ne. Zaben da aka soke na shekarar 1992 an yi tikitin musulmi da musulmi, inda Abiola da Kingibe suka yi takara a karkashin jam’iyyar SDP. Kafin takarar MKO, akwai takarar da aka yi na Kirista da Kirista a jamhoriya ta biyu a shekarar 1979, inda Cif Awolowo ya tsaya takara da abokin takararsa, Philip Umeadi, sai kuma Azikiwe na jam’iyyar NPP da abokin takararsa, Ishaya Audu. Dukkaninsu sun tsaya takara inda Shagari da Ekwueme da suke da tikitin musulmi da Kirista suka sami nasara.