Sojojin Burkina Faso sun ceto Mata 66 da ‘yan ta’adda suka sace

0
110

Mahukuntan Burkina Faso sun sanar da nasarar ceto Mata da kananan yara 66 wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su cikin makon jiya a arewacin kasar.

Sanarwar nasarar ceto Matan 62 da kananan yara 4 da aka bayyana ta gidajen talabijin din kasar sun ce dakarun Sojin kasar ne suka ja tunda da ‘yan ta’addan tare da gwabza fada gabanin ceto fararen hular a jiya juma’a.

Sa’o’I kalilan bayan sace matan ne tawaga ta musamman daga rundunar Sojin kasar ta bazama dazuka don kwato daga hannun ‘yan ta’addan wadanda ke kaddamar da mabanbantan hare-hare a sassan kasar musamman arewaci tare da kisan tarin fararen hula da sunan jihadi.

Gidajen talabijin yayin labaransu na daren jiya juma’a sun rika nuna hotunan matan 62 da yara 4 wadanda aka dawo da su birnin Ougadougou.

A ranakun alhamis da juma’a na makon jiya ne ‘yan ta’addan suka sace matan a yankin Arbinda na arewacin kasar lokacin da suke kan hanyarsu ta neman abinci ga iyalansu.

Wasu rahotanni sun ce an yi nasarar ceto matan ne a yankin Tougouri da ke gab da tsakiyar kasar tazarar kilomita 200 da kudanci gabanin a dakkosu a jirgi zuwa birnin Ougadougou don ganawa da shugabancin Sojin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here