Manoma da ‘Yan kasuwa a jihar Ogun sun tafka asarar biliyoyin naira sakamakon wasu gobara guda biyu da aka yi a cikin mako na biyu a wannan sabuwar shekarar.
Ranar Talatar da ta gabata wasu manoma da ke zaune a garin Siun,karamar hukumar Obafemi Owode,suka bayar da rahoto kan tafka asarar sakamakon mummunar gobara da ta afka musu.
Gobarar ta kai fiye da awa hudu tana ci, kafin a fara samo kanta.
Daya daga cikin manoman da suka yi asara a wannan gobara akwai tsohuwar jakadar Nijeriya a kasar Zambiya da Malawi, Misis Folake Marcus-Bello, wadda gonarta ta kwakwa mai fadin hekta 10 da wasu amfanin suka kone.
Tsohuwar jakadar ta ce ta kashe miliyoyin naira a wannan gona mai suna Folake B Farm wanda kuma dukkansu ta yi asararsu.
“Wannan asarar na sosa min zuciya kwarai da gaske. Ni ban ma san abin da zan ce ba”.
Bayan waccan gobarar da kwana biyu sai ga wata ta sake tashi a kasuwar Odi Olowo da ke Sabo, Shagamu wadda ita ma ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin naira.
In dai za a iya tuna wa dai, an taba yin irin wannan mummunar gobara a wannan kasuwa a cikin watan Janairu na shekara ta 2020, wanda kuma bayan faruwar wannan lamarin gwamnatin jihar Ogun ta gyara ta.
A kaeshe, wadanda wannan gobara ta shafa, sun roki gwamnatin jihar da ta tallafa musu.