Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun ceto ‘yan firamaren da aka sace a jahar

0
105
CHICAGO, ILLINOIS - OCTOBER 19: Chicago police officers patrol downtown as the city celebrates the Chicago Sky's WNBA title on October 19, 2021 in Chicago, Illinois. The city has started to place police officers on unpaid leave for refusing to comply with the city's requirements that they report their COVID-19 vaccination status. Only about 65 percent of the city's police have complied with the order. (Photo by Scott Olson/Getty Images)

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya ta sanar da nasarar kwato yara biyu cikin guda 6 ‘yan makaranta da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar juma’ar da ta gabata.

Idan dai mai saurare zai iya tunawa mun baku labarin yadda ‚yan bindiga suka kutsa kai makarantar Firamare ta garin Alwaza dake karamar hukumar Doma a jihar ta Nasarawa suka yi awon gaba da kananan yara dalibai su 6.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Rahman Nansel ya tabbatarwa da manema labarai cewa kawo yanzu jami’an tsaro na samun bayanai daga daliban da nufin gano hanyoyin da za’a bi wajen kwato sauran yaran da suka rage a hannun ‘yan bindigar.

A cewar sa rundunar hadin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda da kuma ‚yan bijilanti karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mai yaki Muhammad Baba ne suka kutsa cikin daji sannan suka gano yaran guda biyu dukannin su mata da shekarun su basu wuce 6 ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here