Madagascar: Ambaliya ya wanke gidaje 700 bayan mahaukaciyar guguwa ta musu kaca-kaca

0
77

Mahaukaciyar guguwar da ta afka wa garin Sambawa na Madagascar na ci gaba da barna, bayan ambaliyar Ruwan da guguwar ta haddasa wadda ta shafe garin baki daya.

Bayanai sun ce tun ranar Juma’a da guguwar da aka yiwa take da Chabeso ta fara har kawo yanzu garin na Sambawa na karkashin ruwa saboda ambaliyar da ta faru.

Ma’aikatar jin kadi da takaita aukuwar ibtila’i ta kasar ta tabbatar da batan mutum guda, sannan sama da mutane 300 sun bar garin, yayin da gidaje fiye da 700 suka rushe.

Wannan ce mahaukaciyar guguwa ta farko a kakar 2022-23, waddac aka saba yi daga watan Oktoba zuwa Afrilu.

An ci gaba da zabga ruwan sama kamar da bakibb kwarya, amma ana ganin gugwar na raguwa ainun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here