Ana zargin sojojin Najeriya bisa kisan Fulani makiyaya 39 a jihar Nasarawa

0
99
Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

A wani harin bam da ake zargin sojojin kasar nan da kaiwa ya yi sanadiyyar mutuwar Fulani makiyaya akalla 39, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a wani kauye da ke jihar Nasarawa a yankin tsakiyar kasar.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, Maiyaki Muhammad Baba, lamarin ya faru ne a kauyen Rukubi wanda ke daf da iyakar jihar ta Nasarawa da makwabciyarta jihar Benue, inda aka kirga gawarwakin makiyaya 27 da kuma dabbobi masu tarin yawa, koda yake kungiyar Miyetti Allah ta ce, adadin ya kai mutane 39.

Wasu kafafen yada labarai na gida Najeriya sun ruwaito kungiyar da ke kare hakkin makiyaya a kasar wato Miyetti Allah Cattle Breeders Association MACBAN na cewa, jirgin sojojin saman kasar ne ya kaddamar da harin kan makiyaya, batun da har zuwa yanzu sojojin ba su musanta ba ko kuma bayar da bahasi kan dalilin farmakin.

MACBAN cikin wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakinta Muhammad Nura ta bukaci sojojin su bayar da bahasi kan kisan makiyayan wadanda ke kan hanyarsu ta dawowa daga biyan tarar Naira miliyan 29 da jihar Benue ta sanya musu bayan karya dokar kiwo.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule wanda ya sha alwashin gudanar da binciken kan lamarin ya ce, an yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai harin na ranar Laraba wanda ya kashe makiyaya 38 baya ga tarin shanunsu.

Gwamnan ya bukaci kwantar da hankula a yankin da lamarin ya faru wato kan iyakar jihohin Nasarawa da Benue, yankin da ake yawan samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here