Dan takarar gwamna ya rasu a Adamawa

0
126

Dan takarar gwamna a jam’iyyar NRM a Jihar Adamawa, Alhaji Aliyu Maina ya rasu.

Olusola Afuye, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar NRM ne, ya tabbatar da mutuwar Maina.

Mutuwarsa na zuwa kasa da kwanaki 30 kafin babban zabe mai zuwa.

An rawaito cewa ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu bayan gajeriyar jinya da ya yi a Abuja, a ranar ne kuma aka tabbatar da rasuwar dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Jihar Abia, Farfesa Uchenna Ikonne.

“A cewar sanarwar da ‘yan uwan marigayin suka yi, marigayi Alhaji Abba Maina ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja, bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya.

“An yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada, muna addu’ar Allah Ta’ala ya jikansa ya bai wa iyalansa da dukkan masoyansa hakuri,” in ji Afuye.

Yayin da yake kira ga ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da su nuna kulawa da soyayya ga dangin marigayi Maina a lokacin zaman makoki, ya ce za a sanar da jama’a cikakken bayani game da shirye-shirye bayan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here