Mutane 8 din da hukumar ‘yan sanda ke tuhuma a Zamfara

0
80

Rundunar jami’an tsaron da ke yaki da tsageru ta ce, ta kama mutum biyu da ake zarginsu da yin luwadi da kuma wasu mutum shida da ake zarginsu da yin satar wayoyi da kuma fashi da makami.

Shugaban kwamitin rundunar tsaron, Bello Bakyasuwa, ne ya bayyana haka, a wani jawabi da ya gabatar a Gusau.

Bakyasuwa ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargi da yin luwadin ne a Tudun Wada da ke Gusau.

Wanda aka Kaman ya tabbatar da laifin da ake zarginsa da yi na luwadi tare da wani yaro mai shekara bakwai.

Wani daga cikin wadanda ake zargin da aikata wannan badala wanda kuma yake sayar da karas shi ma ya shiga hannu, wanda shi kuma yake yaudararar almajirai a cikin garin Gusau.

Wanda aka kaman ya kware wajen yin luwadin da almajirai.

Kamar yadda ya ce, sauran guda shidan da ake zargin su wadanda aka kama su lokacin taron da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP yin kamfen a Kaura Namoda sauran kuma an kama su a Gusau da laifin rike miyagun makamai da kuma satar waya.

Dukkan wadanda aka Kaman sun amsa laifinsu lokacin da ake yi musu tambayoyi.  Sannan ya kara da cewa,sannan laifin ya saba wa umarnin da gwamna Bello Matawalle ,ai lamba lamba 11na haramta  daba  da shaye-shaye da dykkan wasu miyagun kaifuka.

Bakyasuwa, ya kara da cewa, dukkan wadanda aka Kaman za a gurfanar da su gaban kotu domin yi mudu hukuncin da ya kamata.

Saboda haka sai ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da ba jami’an hukumar hadin kai, wajen ganin an kawo karshen aikata miyagun laifuka a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here