An fara sayar da sabbin takardun Naira a Zaria

0
102
Naira
Naira

Duk da karancin sabbin takardun naira da aka sake yi wa fasali, an ga wasu na sayar da bandir ɗin kuɗin a tashar motar Dadi da ke Sabon Gari-Zariya a Jihar Kaduna kan farashi mai tsada.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ga bandir-bandir na nau’o’i daban-daban na kuɗaɗen da aka baje kolinsu a kofar tashar mota ta Dadi, a unguwar Kwangila a cikin birnin Zariya don masu son saye.

Wani bincike da NAN ta yi ya nuna cewa a na sayar da bandir din Naira 200 na akan Naira dubu 30, Ana siyar da takardun N500 akan Naira dubu 70 sannan ana siyar da ƴannN1,000 akan Naira dubu 130, N100 kuma akan N16,000.

Wani mai sayar da kuɗin, Mohammed Bello, ya ce sai da su ka biya tsakanin Naira dubu 70 zuwa Naira dubu 130 kafin su samu sabbin takardun kudi na Naira dubu 500, ya danganta da nau’in takardun kuɗin da mutum ya ke so.

Sai dai Bello ya ki bayyana inda aka samu kudaden.

Wani mazaunin kauyen Gozaki da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina, Thomas Damina, ya tabbatar wa NAN cewa ya sayi bandir din sabuwar takardar Naira N200 a kan Naira 25,000.

Ya ce an tilasta masa sayen kudin ne kuma da tsada kudi domin ya samu damar sallamar ma’aikatan da ke masa aiki a gona.

NAN ta kuma lura cewa cinikin sabbin takardun Naira ɗin na samun karbuwa, yayin da kwastomomi ke cinkoso a bankuna domin gaggawar ajiye kuɗi kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu.

Daily Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here