Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram Abu Iliya, da wasu 32

0
100
Sojoji
Sojoji

Sojojin Operation Hadin Kai tare da dakarun hadin gwiwa na farar hula sun hallaka wani babban kwamandan Boko Haram, Abu Illiya tare da mayakansa 32.

An ce an samu nasarar hakan ne a yayin wani sintiri da jami’an leken asiri suka kai a wasu kauyukan Kayamari, Habasha da Yuwe da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, majiyoyin leken asiri da dama sun nuna cewa, karfin wutar da sojojin ke da shi ya tilasta wa ‘yan ta’addan da suka tsira tserewa cikin rudani ta yadda suka yi watsi da dukiyoyinsu da makamansu.

Sojojin sun kuma gano tare da lalata kekuna 50 daga maboyar ‘yan ta’addar.

Sabon Kwamandan Theatre, Joint Task Force, Operation Hadin Kai na Arewa maso Gabas, Manjo Janar Ibrahim Ali jim kadan bayan karbar ragamar hukumar ya yi alkawarin ci gaba da kokarin kawo karshen yakin da Boko Haram ke yi a yankin Arewa maso Gabas.

Don cimma wannan, a cewar sabon kwamandan, dole ne a hada karfi da karfe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here