A karo na 5, Akwa Ibom ta kara lashe kambun jiha mafi tsafta a Najeriya

0
251

A karo na iyar a jere, Akwa Ibom ta sake lashe kambun Jihar da ta fi kowace tsafta a fadin Najeriya.

Shugaban Hukumar Kwashe Shara da Kare Muhalli ta Jihar, Prince Akpan Ikin ne ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da kambun ga Gwamnan Jihar, Udom Emmanuel, yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar a Uyo, babban birnin Jihar.

Shugaban ya alakanta nasarar da tallafin da Gwamnan ke ba hukumar ba dare ba rana.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar.

A cewar sanarwar, “Gwamna ya jinjina wa hukumar kan irin hobbasan da suke yi wajen yin aikinsu tsakani da Allah, wanda shi ne ma sirrin da Jihar ta samu nasarar kare wannan kambu tsawon shekara biyar a jere.”

Kazalika, Kwamishinan ya ce Gwamnan ya kuma hori mambobin Majalisar Zartarwar tasa da su dada zage damtse wajen kammala muhimman ayyukan da suka saka a gaba, kasancewar wa’adin gwamntin ya zo karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here