Wata mata ta saci daya daga cikin tagwayen da aka haifa a asibitin Kano

0
118

Wata mata da har yanzu ba a tantance sunanta ba ta sace wa mahaifiya wasu tagwaye da ta haifa bayan ‘yan awanni da haihuwa a asibitin Abdullahi Wase da ke Kano.

Rahotanni sun ce an ja tagwayen daga hannun mahaifiyarsa a daya daga cikin dakin aikin na asibitin.

Mahaifiyar, Hajiya Aisha Abubakar, matar dan jaridan Kano, Muhammad Auwal Tudun Murtala, ta haifi tagwayen ne da misalin karfe 12 na ranar Lahadi lokacin da lamarin ya faru.

Da yake mayar da martani kan lamarin, mijinta Muhammad Auwal ya bayyana cewa ya rubutawa sashin tsaro na Asibitin kuma ya tuntubi ‘yan sanda.

Karin bayani na nan tafe

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here