Ana shiryawa Tinubu zagon kasa a fadar Aso Rock don ya fadi zabe – El-Rufa’i

0
117

Gwaman jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yace akwai wasu “jami’ai” a fadar gwamnatin Najeriya ta Aso Rock dake Abuja dake wa dan takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasar Asiwaju Bola Tinubu, zagon kasa domin ya fadi zabe.

Da yake magana a wani shirin safe na gidan Talabijin na Channels, gwamnan ya ce wadannan mutanen da bai bayyana sunayensu ba suna cike da takaicin yadda Tinubu ya doke ‘yan takararsu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, abin da ya sa suka shiga shirya makarkashiya domin ya fadi zabe.

El-Rufai ya ce mutanen na fakewa ne da muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin abin da yake ganin ya dace.

“Suna kokarin ganin lallai sai mun fadi zabe, kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace. Zan ba da misali guda biyu: wannan tallafin man fetur da ake kashewa tiriliyoyin Naira, tuni muka amince a janye”.

Malam Nasir El-Rufai yace yayi wata tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021, inda ya nuna masa illar dake cikin ware sama da Tiriliyan 2 wajen biyan tallafin man fetur alhali kuwa ana kashe Naira biliyan 200 kacal a kasafin kudin gudanar da manyan ayyuka.

Yace shugaban kansa ya gamsu, hakan kowa dake cikin gwamnati ya amince da batun cire tallalfin.

Buhari ne ya sauya fasalin kudi

Misali na biyu da Gwamna El-Rufai ya bayar shine batun sauya fasalin wasu takardun kudin Najeriya Naira. Yace ana daurawa gwamnan babban bankin Najeriya CBN wannan laifi, amma kuma ba haka bane.

“Jama’a na zargin Gwamnan Babban Bankin ne da laifin sake fasalin kudin, amma ba haka batun yake ba, ku tuna da mulkin Buhari na farko a soji; wato gwamnatin Buhari da Idiagbon sun canza mana kudin mu kuma sun yi haka a asirce da nufin kamo wadanda ke wawure kudaden haram”.

Yace hakan mataki ne mai kyau, kuma hakkin sa ne, to amma yin hakan a wannan lokaci bashi da ma’ana a fuskantar tattalin arziki da siyasa.

Kalaman El-Rufai na zuwa ne mako guda bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki Asiwaju Bola Tinubu yayi zargin ana shirya makarkashiya don hanashi samun nasara a zabe mai zuwa ciki harda tsadar mai da kuma batun canjin kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here