Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umurci ilahirin bankunan da ke jiharsa, da su raba sabbin takardun naira ta hanyar na’urorin ATM da kuma biya ta kan kanta, ko kuma gwamnatin sa ta kwace filayen su.
Zulum ya yi wannan gargadin ne bayan da ya ziyarci rassan bankuna da ke birnin Maiduguri, domin tantance matsalolin da mazauna yankin ke ciki dangane da neman samun sabbin takardun kudin Naira.
Gwamnan ya bayyana bacin ransa kan yadda ya ga daruruwan mutane sun yi layi a reshen wani banki inda na’urar ATM guda daga cikin 10 kawai ke bayar da kudi.
‘Yan Najeriya a sassan kasar dai na cigaba da shan wahalar neman sabbin kuddaden naira har ma da tsaffin da yanzu suka yi karanci, yayin da kuma a lokaci guda suka fama da matsalar karancin man fetur.