Mahaifin da ya haifi yara 102 tare da matan sa 12, da kuma jikoki 578

0
111

Wani mazaunin yankin karkarar kasar Uganda Musa Hasahya Kasera, yace ya gaji da haihuwa haka, saboda haka akai kasuwa, bayan ya haifi yara 102 tare da matansa guda 12, abinda ya kai shi samun jikoki 578.

Hasahya dake kauyen Bugisa a Yankin Butaleja ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar ganin yadda halin lafiyarsa ke tabarbarewa da kuma eka 2 kacal na filin noman da ya mallaka, ya zama dole ya sake nazarí akan rayuwarsa, musamman ganin 2 daga cikin matansa sun gudu.

Mutumin mai shekaru 68 da yanzu haka bashi da wani aikin yi, ya mayar da kauyensu wajen yawon bude ido ga baki wadanda ke tattaki domin gani da idonsu shin wannan lamari haka yake da gaske, yayin da sauran matansa ke shan maganin hana daukar ciki.

Hasahya yace babu tantama matansa na shan maganin hana daukar ciki amma shi baya sha, duk da yake baya fatar samun Karin haihuwa saboda ya fahimci kuskuren da yayi wajen haifan yaran da ba zai iya daukar nauyin su ba.

Shidai wannan magidanci yayi auransa na farko ne a shekarar 1972 lokacin wani bikin gargajiya, yayin da yake da shekaru 17 da haihuwa a duniya, abinda ya kai shi samun ‘yarsa ta farko Sandra Nabwire shekara guda bayan auran.

'Ya'yan Musa  Hasahya yayin wasanni a filin gidansu da ke yankini Butaleja a Uganda.

Saboda su biyu kadai mahaifiyarsu ta haifa, ya sa wansa da danginsa suka bukace shi da ya kara auro wasu mata domin samun yara da yawa da zasu fadada danginsu.

Hasahya yace wannan ta sa ya gamsu da shawarar da aka bashi a matsayinsa na dillalin shanu kuma mahauci inda ya dinga kara mata har wadanda suke kasa da shekaru 18.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace yaran Hasahya 102 na tsakanin shekaru 10 ne zuwa 50, yayin da matarsa mafi karancin shekaru ke da shekaru 35 a duniya.

Hasahya ya ce baya iya tuna sunayen da yawa daga cikin yaran nasa in banda babbansu da ‘dan autansu, abinda ya sa uwayensu mata ke tuna masa sunayensu.

Wani abin takaici shine wannan mutumin baya iya tuna sunayen wasu daga cikin matansa har sai ya tintibi daya daga cikin ‘yayansa Shaban Magino mai shekaru 30 wanda ke aikin koyarwa a makarantar firamare, yake kuma taimakawa wajen tafiyar da al’amuran gidansu a matsayinsa na daya daga cikin yaran gidan da suka samu ilimi.

Domin warware rikice rikicen da suka taso a tsakanin iyalan gidan, Hashaya yace su kan gudanar da taron wata-wata a tsakaninsu.

Wani jami’in karamar hukumar yankin dake kula da Bugisa, kauyen dake dauke da mutane kusan 4,000 yace duk da matsalolin da ake fuskanta, Hasahya na baiwa ‘yayansa tarbiya ta gari, kuma babu matsalar sata ko kuma fada a tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here