Manoman kwakwa 50 sun samu horo kan noman zamani

0
124

A kokarin da ake yi na kara habaka noman kwakwar manja na zamani a kasar nan, ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta tarayya, ta horas da manoman kwakwa da masu sarrafa ta su hamsin a jihar Edo.

A jawabinsa a wajen kaddamar da horon, ministan ma’aikatar Dakta Mohammad Abubakar ya bayyana cewa, horon na daya daga cikin shirin gwamnatin tarayya na samar da wadataccen abinci a kasar nan.

Abubakar ya ci gaba da cewa, horaswar na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na inganta rayuwar manoman na kwakwar manajan da kuma masu sarrafa ta a kasar nan, sannan ya ce, a taron horaswar, za a kuma ilimantar da mahalarta taron dabarun zamani na noman kwakwar, musamman yadda za su ci gaba da yin nomanta sosai.
Ministan wanda darakta a ma’aikatar ta aikin noma Chukwuemeka Ukattah ya wakilce shi, ya bayyana cewa, ma’aikatar za ta kuma horas da wasu ma’aikan ma’aikatar a kan renon irin kwakwar manajan, musamman domin su dinga noma wadda za ta samu karbuwa a kasuwar duniya.

Shi ma a na sa jawabin, a gurin taron darakta a cibiyar gusanar da binciken kan irin na kwakwar manajan ta kasa NIFOR Dakta Celestine Ikuenobe ya bayyana cewa, kwakwar manajan da ake noma wa a kasar nan, ba ta isar kasar nan.

Shugaba Celestine ya ci gaba da cewa, idan kungiyar manoman kwakwa ta kasa da kuma kungiyar masu safarar kwakwar sun bayar da hadin kai noman na kwakwar zai iya taimaka wa matuka wajen kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.

A cewar Celestine, ana ci gaba da nuna bukatar ta irin kwakwar manajan a kasar nan, musamman a cikin shekara uku da suka gabata, saboda karin bukatar kwakwar a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here