Kotun koli ta bai wa Ahmad Lawan takarar sanatan Yobe ta arewa

0
155

Kotun Koli ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan matsayin halastaccen ɗan takarar kujerar sanata ta Yobe ta arewa.

Da yake yanke hukuncin alƙalin kotun mai shari’a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Damaturu hujjar – baka ta zargin aikata maguɗi a zaɓen fitar da gwanin – da ya sa ake gayyatar ɓangaren Ahmad Lawan zuwa kotun.

Jam’iyyar APC ce dai ta ƙalubalanci Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ɗan takara.

A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen, inda a cewarsa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

Sanata Ahmad lawan dai bai shiga takarar fitar da gwani na farko da jam’iyyar ta gudanarar ranar 28 ga watan Mayun 2022, kasancewar ya shiga takarar shugabancin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here