Malami ya umarci kotun koli ta Najeriya tai watsi da karar da gwamnonin arewa suka shigar akan janye wa’adin karbar tsohon kudi

0
103

Babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bukaci kotun kolin kasar da ta yi watsi da karar da wasu gwamnatocin jihohin arewacin kasar guda uku suka shigar, suna kalubalantar wa’adin da babban bankin Najeriya ya sanya a ranar 10 ga watan Fabrairu na kawo karshen batun karbar tsofaffin takardun naira.

Ta hannun lauyoyinsa Mahmud Magaji da Tijanni Gazali Gwamnatin tarayya ta ce kotun kolin ba ta da hurumin sauraran karar

Don haka, gwamnatin tarayya na neman kotun kolin ta soke karar saboda rashin hurumi.

A cikin karar da aka shigar a kotu ranar 8 ga Fabrairu, 2023, AGF ta ce “masu gabatar da kara ba su nuna dalilin da ya dace na gabatar da kara ba.”

A ranar 3 ga watan Fabrairu ne gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka maka gwamnatin tarayya kara kan batun sauya fasalin naira na babban bankin Najeriya CBN.

Da take yanke hukunci a kan bukatar da masu shigar da kara suka gabatar, Kotun Koli ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da manufar sake fasalin kudin har sai an yanke hukunci.

Jihohin sun bukaci kotun koli ta tilasta wa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), CBN da kuma bankunan kasuwanci da su janye wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na tsohuwar takardar kudi na N200, N500 da N1,000 a matsayin kudin shiga na Najeriya.

Sai dai kuma lauyoyin da ke kare karar sun bayar da hujjar nuna goyon bayansu ga kin amincewar da aka yi, dogaro da sashe na 251 na kundin tsarin mulkin kasar, lauyoyin da ke kare masu kara sun ce karar na da hurumin domin karar ta na cikin sashen da ke magana akan harkokin kudi na gwamnatin tarayya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here