Kotu ta kori Mohammed Abacha daga takarar gwamnan Kano

0
97

Kotun Daukaka Kara ta kwace takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP daga Mohammed Sani Abacha ta bai wa Sadiq Aminu Wali.

A zaman kotun da ke Kano ranar Juma’a, alkalan sun soke hukuncin Babbar Kotun da ta ayyana Mohammed Abacha a matsayin halastaccen dan takarar PDP.

A hukuncin alkalan kotun su uku, wanda Mai Shari’a Usman Musale, ya karanta sun umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dauke shi a matsayin halastaccen dan takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP.

Kafin zuwa Kotun Daukaka Karar, Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha a matsayin dan takarar Gwamnan Kano na PDP a zaben 2023, bayan Mai Shari’a A. M. Liman, ya soke zaben fid-da gwanin da ya samar da Sadiq Wali a matsayin dan takarar Gwamnan na Kano a PDP.

A lokacin, kotun ta umarci INEC da ta maye gurbin Sadiq din da Mohammed Abacha.

Idan za a iya tunawa, a lokacin da PDP ke fama da rikicin cikin gida a Jihar Kano, kowanne daga bangarorin jam’iyyar guda biyu ya gudanar da zaben fid-da gwani, lamarin da ya sa aka samu ’yan takarar guda biyu Sadiq Wali da Mohammed Abacha.

Kowannensu na ikirarin cewa shi ne halastacce, lamarin da ya kai su gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here