Bwacha ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan APC a Taraba

0
88

Sake zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Taraba na jam’iyyar APC, ya sake haifar da Sanata Emmanuel Bwacha, a matsayin wanda ya lashe zaben kuma dan takarar jam’iyyar.

Zaben wanda aka gudanar cikin ruwan sanyi a yau a Jalingo babban birnin jihar, tsohon babban hafsan sojin kasa (COAS), Janar Tukur Bruratai (mai ritaya) ne ya jagoranta.

Mambobin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro ne suka sanya ido a zaben fidda gwani.

Buratai wanda shi ne shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnan jihar Taraba na jam’iyyar APC, ya bayyana Bwacha a matsayin wanda ya lashe zaben baki daya, bayan da ya samu kuri’u 778 inda ya doke sauran ‘yan takara biyar.

Buratai ya kara da cewa yayin da aka samu kuri’u 796 da aka tantance, jimillar wadanda suka kada kuri’a 835 ne da kuri’u 783. Ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da suka ji haushin kayi da su rungumi kaddara.

Ya kuma bukaci sauran ‘yan takarar da su hada kai da mai rike da tutar jam’iyyar domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP mai mulki a zabe mai zuwa.

A baya-bayan nan ne dai kotun kolin ta soke zaben fidda gwanin da aka gudanar a baya wanda ya samar da Bwacha, sanata mai wakiltar Taraba ta kudu a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here