Wani ya rasu yayin da magoya bayan APC da PDP suka yi arangama da juna a Jigawa

0
109

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 37 mai suna Abdullahi Isiyaku, yayin da wasu da dama suka jikkata a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan PDP da APC a karamar hukumar Maigatari.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa Leadership Hausa.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP ke gudanar da wani taro a Maigatari.

Shiisu ya bayyana cewa rikicin ya barke ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar PDP suka isa sakatariyar jam’iyyar APC da ke Gangare, inda suka kai wa wani Abdullahi Isiyaku hari.

Ya ce an garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da shi zuwa Babban Asibitin Gumel, inda daga baya daya ya mutu a lokacin da yake jinya.

Shiisu, ya ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a rikicin.

Ya ce an mika lamarin zuwa ga sashen binciken manyan laifuka (SCID) don yin bincike mai zurfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here