Kotu ta yanke wa malami daurin rai-da-rai kan yi wa yarinya fyade

0
103

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Ikeja, Jihar Legas, ta yanke wa wani malamin makaranta hukuncin daurin rai-da-rai bayan da ta kama shi da laifin yi wa daliba ’yar shekara shida fyade.

Da take yanke hukuncin a ranar Litinin, Mai Shari’a Sedoten Ogunsanya ta ce mai tuhuma ya gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da suka tattabar wanda ake kara ya aikata laifin da ake zargin sa.

“Akwai lokacin da ya kira ta zuwa dakin zane-zane (a makaranta) inda ya dauke ta ya dora a kan tebur ya cire mata kamfai sannan ya.……,” in ji Alkalin.

Bayanan da aka gabatar wa kotun sun nuna wanda ake zargin ya aikata wa yarinyar fyade sau da dama a lokuta daban-daban.

’Yan sanda sun ce an gano abin da ya faru ne bayan da yarinyar ta bai wa mahaifiyarta labarin abin malamain nata ya aikata mata.

Daga bisani dai magana ta bayyana inda iyayen suka kai rahoto ga ’yan sanda, aka shigar da maganar Kotun Majestare da ke yankin Ogudu kan zargin fyade, amma wanda ake zargi ya musanta.

Daga bisani aka tura batun gaban Alkali Sedoten Ogunsanya, bayan shawarar da sashen tuhuma na jihar ya bayar.

Kotun ta nuna rashin gamsuwarta da duka hujjojin da aka gabatar mata daga bangare mai kare kansa, lamarin da ya sa ta yanke wa mailafin hukunci  daurin rai-da-rai a kurkuku.

Lauyan wanda ake kara, O.C. Olagunju ya roki kotun kan ta yi sassauci a hukuncin da ta yanke wa wanda yake karewa.

Shi kuwa lauyan mai gabatar da kara, Jubril Kareem, ya bukaci kotun ta aiwatar da hukuncin kamar yadda doka ta tanada.

A karshe, Alkali Ogunsanya ta yanke wa mai laifin hukuncin daurin rai-da-rai a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here