CBN ne kadai zai ci gaba da karbar N500 da N1,000 — Buhari

0
110

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya(CBN) kadai zai ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 bayan karewar wa’adinsu a ran 10 ga Fabrairu, 2023.

Ya kuma ce, za a ci gaba da amfani da tsohuwar N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu domin rage wa ’yan kasa radadin karancin kudin da ake fuskanta.

“Za ci gaba da amfani da N200 daga ranar 10 ga Fabrairu zuwa 10 ga Afrilu, 2023,” in ji shi.

Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa da ya gabatar kai tsaye da safiyar Alhamis domin sanar da ’yan kasa halin da kasa ke ciki.

Buhari ya ce da izininsa CBN ya canza takardun kudi na N200 da N500 da kuma N1,000.

Shugaban ya nuna damuwarsa kan halin da ’yan kasa suka tsinci kansu dangane da sabbin dokokin CBN, matakin da ya ce an dauka ne domin bunkasa tattalin arziki da yaki da rashawa da yaki da matsalar tsaro da kuma dakile siyasar kudi.

Ya kara da cewa an samu nasarar rage yawan tsabar kudaden da ke yawo a hannun jama’a wanda hakan na daya daga manufar sabbin dokin na CBN.

Buhari ya bukaci CBN ya yi amfani da dukkan hanyoyi da suka sawwaka gare shi wajen wayar da kan ’yan ksa dangane da sabbin dokokin nasa.

Game da sha’anin zabe mai zuwa, Buhari ya bai wa ’yan Najeriya tabbacin gudanar da zabe mai tsafta kuma cikin lumana.

Ya kuma yi kira ga ’yan kasa da su fito lokacin zabe su kada kuri’a cikin lumana.

Ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kare ’yancin Najeriya a matsayin kasa.

Shugaban ya nuna godiyarsa ga ’yan kasa bisa hakuri da juriyar da ’yan Najeriya  suka nuna, tare da yi wa Tarayyar Najeriya fatan alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here