Boko Haram na shirin kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari — DSS

0
96

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS)  ta gano wani shirin kungiyar Boko Haram na kai sabon hari kan jirgin kasan Abuja-Kaduna a ’yan kwanakin da ke tafe.

Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta aike wa Ma’aikatar Tsaro, tana bukatar a dauki mataki.

Ma’aikatar ta ce DSS ta sanar da ita gane da yunkurin harin Boko Haram din ne tun a ranar 1 ga watan Fabrairu da muke ciki.

A kan haka ne ta jaddada bukatar Ma’aikatar Tsaron ta dauki gargadin da muhimmanci tare da kiran taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin shawo kan barazanar harin.

Sabuwar barazanar harin na zuwa ne ’yan watanni bayan dawowar jirgin kasan na Abuja-Kaduna aiki tun bayan harin bom da ’yan bindiga suka kai masa, suka sace kimanin mutum 60 tare kashe wasu kimanin 10.

A jajibirin watan Ramadan na 2022 ne kungiyar ta kai wa jirgin kasan ta da ya baro Abuja da Magariba harin, ’yan kilomitoci kadan kafin ya sauka a Tasharsa da ke Rigas a Kaduna.

Sai da mutanen da maharan suka sace suka shafe wata takwas a hannun ’yan bindigar kafin su sako su, bayan an jima ana kai ruwa rana da kuma matsin lamba da gwamnati ta yi ta sha.

Harin na ranar 28 ga watan Maris ya jawo harkokin sufurin jirgin kasan, wanda galibi mutane kan shiga ne saboda guje rashin kayan hanyar Abuja-Kaduna da kuma matsalar ’yan ta’adda da ke garkuwa da mutane a kan hanyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here