Majalisar dinkin duniya ta kafa gidauniyar dala biliyan 1 don taimakon wadanda girgizar kasa ta shafa a Turkiya

0
99

Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da gidauniyar dala biliyan guda a don taimaka wa wadanda iftila’in girgizar kasar da ta kashe dubban mutane ta shafa a Turkiya.

A wata sanarwa, babban magatakardan majalisar dinkin duniyaAntonio Guterres ya ce za yi  amfani da kudaden da za a tara ne don samar da agaji ga sama da mutane miliyan 5 da iftila’in ya rutsa da su.

Ya kara da cewa kudaden za su taimaka wa kungiyoyin agaji wajen samar da gudummawa ta fannin abinci, ruwan sha, da matsugunai.

Akasarin yankunan da wannan girgizar kasa ta shafa na  cikin matukar bukatar agaji, inda suke fama da rashin abinci, ruwansha da makewayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here