INEC na sa ran karbar sauran kudaden sallamar ma’aikatan ta daga CBN a yau Talata – Okoye

0
100

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙara jaddada cewa ta na da tabbacin karɓar kuɗaɗen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi mata alƙawarin bayarwa a yau Talata zuwa gobe Laraba.

Kuɗaɗen dai su ne waɗanda za a biya wasu ma’aikatan zirga-zirga ko sufurin da tura masu kuɗaɗe ta asusun ajiyar su zai samu cikas, ɓata lokaci, ko kuma wataƙila ma ba su da asusun ajiyar kwata-kwata.

Kwamishina kuma Babban Jami’in Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Festus Okoye, shi ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Lahadi.

INEC ce dai ta roƙi CBN ya tanadar wa hukumar tsabar kuɗaɗe waɗanda za ta biya ayyukan da za ta biya da kuɗi kai-tsaye, ba ta hanyar ‘riransifa’ ba.

Da aka tambayi Okoye lokacin da INEC za ta karɓi kuɗaɗen daga CBN, sai ya ce, “Mu na sa ran cewa za mu magance duk wata matsalar biyan kuɗaɗe daga ranar Talata, 21ga Fabrairu.”

Okoye ya ce ya na ganin tashe-tashen hankulan ƙone-ƙone da ake yi a wasu garuruwa saboda ƙarancin kuɗaɗe bai zai hana mutane yin tururuwar fita su jefa ƙuri’a ba.

Ya ce INEC ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓe sahihi kuma karɓaɓɓe, haka ya ke da yaƙinin cewa ɓangarorin tsaro su ma sun yi na su shirin domin samar da kyakkyawan tsaro a lokacin zaɓe da kuma lokacin tattara sakamakon zaɓe da kuma lokacin bayyana sakamakon zaɓe.

Makonni biyu da su ka gabata ne shugaban INEC ya kai ziyara a Hedikwatar CBN, inda Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya cire masa shakkun samun tangarɗar kuɗaɗen sallamar ma’aikatan zaɓe.

A lokacin ziyarar, CBN ya shaida wa Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, cewa sauya launin kuɗi ba zai shafi zaɓen 2023 ba.

Ya ce CBN zai samar wa INEC dukkan kuɗaɗen da hukumar ke buƙata a lokacin zaɓukan ranar 25 ga Fabrairu da na 11 ga Maris, 2023.

Emefiele ya shaida wa Yakubu cewa a ko da yaushe CBN na goyon bayan INEC ta kowane fanni domin tabbatar da cewa ta gudanar da aikin da aka ɗora wa hukumar a cikin nasara.

Ya ce: “Mu na shiga harkokin ayyukan INEC adanawa da ajiyar kayan zaɓe, har ma da amfani da motocin CBN masu sulke wajen rarraba kayan zaɓe.

“Mu na farin cikin cewa a cikin wannan kyakkyawar alaƙa tsakanin CBN da INEC, ba mu taɓa kawo wa INEC cikas ko dagula masu lissafi ba. Saboda haka ɗin ne ma ba ku gudun mu, ga shi a yanzu ma kun dawo mana a wannan zaɓen.

“Idan shugaban INEC zai tuna, lokacin da na kai maka ziyara a baya, ka tambayi yadda CBN zai samar wa INEC kuɗaɗen waje domin sayen na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS), da sauran kayan aikin zaɓe. Na ba ka tabbacin za a samar, kuma an samar ɗin.

“Saboda haka CBN ba zai bari a yi amfani da shi ba wajen kawo wa zaɓen 2023 cikas.

“Don haka ina tabbatar maka idan ka na buƙatar takardun kuɗaɗe domin biyan motocin sufuri kuɗin su a hannu, bayan ka yi biya ta tiransifa, to CBN a shirye ya ke ya bayar.”

Tun da farko, Yakubu ya nemi haɗin kan CBN domin tabbatar da zaɓen 2023 cikin nasara, musamman ganin yadda ake ta haƙilon ƙarancin kuɗaɗe kusa da zaɓe.

Yakubu ya ce INEC ta yi shiri tsaf domin tabbatar da zaɓen 2023 ya zama sahihin zaɓen da a tarihi ba a taɓa yin kamar sa ba a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here