Kotu ta kori karar da aka shigar kan tsige shugaban ‘yan sanda na kasa

0
101

Mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ya yi watsi da karar da ke neman sauke babban sufeton ‘yan sanda, IGP Alkali Baba Usman daga matsayinsa.

Kotun ta yi watsi da karar da wani mai rajin kare hakkin Jama’a, Micheal Sam Idoko ya shigar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu mutane hudu, sabida rashin caccantar karar.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotoso ya yi amfani da sashe na 7 (6) na dokar ‘yan sanda ta shekarar 2020 wanda ya sanya wa’adin kowane Sufeto Janar na ‘yan sanda yayi shekaru hudu a kan mukaminsa.

Alkalin kotun ya ce ritayar Alkali Baba Usman daga aikin ‘yan sandan Nijeriya ba ta da alaka da nadin da aka yi masa, wa’adin shekaru hudu na ofis yana nan da sahihancinsa.

Baya ga haka, Mai shari’a Omotoso ya ce wanda ya shigar da karar da ya yi ikirarin cewa, shi mai rajin kare hakkin al’umma ne, ba shi da hurumin shigar da kara a madadin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here