Kasar Amurka ta yi kira da a tabbatar da an gudanar da zaben Najeriya da za a yi cikin lumana, inda ta ce zaben ya shafi duniya baki daya.
A cikin wani bidiyo da Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken da wasu masu ruwa da tsaki na kasar suka aike wa Aminiya, Amurka ta bukaci ’yan Najeriya da su fita su kada kuri’a don zabar wanda suke so.“A lokacin zaben, ku ’yan Najeriya kuna da damar bayyana muryoyinku don a ji ku ta hanyar zabar shugaban da zai mulke ku.
“Zabenku na da muhimmanci ba a gare ku kadai ba, har ma da duniya baki daya,” in ji Blinken.
Har wa yau, Amurka ta jadadda cewar ba ta goyon bayan kowane dan takara a zaben da za a shiga a ranar Asabar, bukatarta kawai shi ne a gudanar da zabe cikin lumana.
Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumomi daga ciki da wajen Najeriya ke ci gaba da kirayen-kiranye da sanya ido kan yadda zaben zai gudana.